Sanata Ibrahim Khalid

“An zabe ni domin ma Jama’a Hidima, Tare da Chigaban Mazaba ta. “Sanata Mai Wakiltar Yankin Kaduna ta 1”

Gundumar L. G.

Sanata Barr. Ibrahim Khalid

“Sanata Ibrahim Khalid Mustapha fitaccen ɗan siyasa ne na Nijeriya kuma jigon yiwa jama’a hidima, haifaffen Karamar Hukumar Soba, a Jihar Kaduna. A yanzu haka shi ne wakilin Gundumar Sanata ta Kaduna Arewa a Majalisar Dokoki ta 10, wanda ya fara aiki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023. bayan nasarar da ya samu a zaɓen Nijeriya na shekarar 2023.”

 

Kudurori da Dokoki

A matsayin babban majalisar dokoki a ƙasar nan, Majalisar Dattawa (Red Chamber) na da ikon da Kundin Tsarin Mulki ya tanadar mata, na tsara dokoki domin zaman lafiya, oda, da kyakkyawan shugabanci a Tarayyar Najeriya. Haka kuma, tana da ikon wakiltar muradun jama’a, fatansu, burinsu da kuma kula da walwalarsu. Baya ga haka, wannan babbar majalisar tana da alhakin bincikar hukumomin gwamnati da ma’aikata domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin mulki.

"Ina Tare da Kai a Kowane Mataki"

"A bisa Jagoranci mai Cike da Manufa."