Sanata mai wakiltar Yankin Kaduna ta 1

Sanator Ibrahim Khalid Mustapha

Sanata Ibrahim Khalid Mustapha Kamilin dan siyasa ne mai son jama’a, kuma wanda jama’a ke so. An haife shi a Ƙaramar Hukumar Soba da ke Jihar Kaduna. A halin yanzu, yana wakiltar Mazabar Sanata ta Kaduna Arewa a Majalisar Dattawa ta 10, bayan ya hau kujerar ne a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, bayan nasarar da ya samu a zaɓen gama gari na Najeriya na 2023.

Sanata Mustapha, memba ne na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), kuma yana amfani da ƙwarewar sa na shekaru da dama a harkar siyasa cikin aikinsa. Zaben sa a matsayin sha na dan siyasa mai wakiltan jama’a a gwamnati ya fara ne ta Majalisar Wakilai, inda ya wakilci Ƙaramar Hukumar Soba daga shekara ta 2007 zuwa 2015, a lokacin Majalisar ta 6 da ta 7. Jagorancin sa ya kasan ce cike da tsara dokoki masu amfani da kuma aiwatar da shirye-shiryen ci gaban al’umma.

A zaɓen fidda gwani na PDP, Sanata Mustapha ya nuna basirarsa a siyasa da goyon bayan jama’a ta fuskoki daban-daban, inda ya samu ƙuri’u 257 da suka ba shi nasara don tsayawa takarar wakiltar Kaduna ta Arewa a Majalisar Dattawa.

Gudunmuwar Doka da Ayyukan Kwamitoci

A matsayin sa na Sanata, Ibrahim Khalid Mustapha na aiki a cikin muhimman kwamitoci da dama, ciki har da Kwamitin Hali, Dokar Da’a da Ƙorafe-ƙorafe na Jama’a, inda yake aiki tare da abokan aikinsa domin tabbatar da gaskiya, adalci, da ingantacciyar bunkasa harkar dokoki a Najeriya.

“Karfafa Ci gaba a Mazabar Kaduna ta Daya”

Sanata Ibrahim Khalid

“Ya jajirce ba tare da kasala ba wajen inganta walwalar mutanen mazabar sa, da kuma karfafa ci gaba mai ɗore wa a fadin Kaduna ta Arewa. Manyan abubuwan da ya fi maida hankali a kansu sun haɗa da”

Harkan Ilimi

Sanata Ibrahim Khalid Mustapha ya jajir ce matuka wajen sauya fasalin fannin ilimi a Kaduna ta Arewa. Ya sanya gyare-gyaren makarantu da ɗaukaka su zuwa na zamani a sahun gaba, tare da samar da kayayyakin koyarwa na zamani da tabbatar da cewa cibiyoyin ilimi sun samu duk abin da ake buƙata domin ɗalibai da malamai su yi aiki yadda ya kamata. Ganin cewa ilimi shi ne ginshiƙin ci gaba, yana tallafa wa Dalibai, da shirye-shirye da dama a bisa manufar rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, inganta horar da malamai, da faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi musamman ga al’ummomin da ake bari baya."

Inganta Ababen More Rayuwa

Inganta hanyoyin mota, gadoji da sauran muhimman ababen more rayuwa domin haɓaka ci gaban tattalin arziki da sauƙaƙa zirga-zirga a mazabun sa baki daya. Ilimi da Lafiya: Sabunta makarantu, asibitoci da cibiyoyin al’umma domin samar da ingantattun ayyuka ga jama’a.

Inganta Harkar Noma

Tallafa wa manoma ta hanyar basu horo, kayan noma, da na'urorin zamani domin ƙara yawan amfanin gona samar da wadatan amfanin gona mai yawa.

Kara Wa Matasa Kwarin Gwiwa

Bukasa wa da shirye-shiryen da ke koyar da matasa wajen ƙwarewa, da basu damar shiga harkokin kasuwanci, da samar da hanyoyin dogaro da kai domin samun aikin yi. Sanata Jagora Mai Hangen Nesa kuma Mai tallafawa Matasa da Jama’a.

Health Care

In the area of healthcare, Senator Mustapha works tirelessly to improve access to quality medical services for his constituents. He advocates for the upgrade of existing hospitals and clinics, the establishment of new healthcare centers in underserved areas, and the provision of modern medical equipment and supplies. Additionally, he supports initiatives that address maternal and child health, promote preventive healthcare, and improve the overall wellbeing of the community through awareness campaigns and partnerships with health organizations. As part of his commitment to empowering the youth through education, Senator Mustapha provides financial support by awarding school fees to students at various levels, from primary to tertiary institutions. Additionally, he has established scholarship programs that grant opportunities for exceptional students to further their education, both nationally and internationally. Through these initiatives, he continues to foster academic excellence and ensure that no deserving student is denied an education due to financial constraints.

Sanata Ibrahim Khalid Mustapha

Sanata Ibrahim Khalid mutum ne mai kokarin hada kan jama’a, wanda ke aiki tukuru domin daidaita bukatun mazabar sa da manufofi da kuma shirye-shiryen gwamnatin tarayya masu tasiri. manufofin sa na nuna cikakken fahimta game da gudanar da mulki da kuma kishin kawo sauyi wadan da za su inganta rayuwar al’umma. Ta hanyar hadin gwiwa da jam’iyyar PDP da manyan masu ruwa da tsaki, Sanata khalid yana matukar jajircewa wajen jawo ayyukan ci gaba a mazabar sa ta Kaduna Zone 1.