"Gudummawar Dokoki ta Sanata Ibrahim Khalid a Majalisar Tarayya ta 10."

Sanata Ibrahim Khalid, wakilin da ake Alfahari da shi a Shiyar Kaduna Zone 1, ya nuna cikakken jajircewar sa wajen kula da jin daɗin jama'a da ci gaban al’ummarsa, ta hanyar ƙoƙarin ƙirƙirar dokoki masu amfani. A tsawon zaman sa a Majalisar Tarayya ta 10, Sanata Khalid ya jagoran ci gabatar da muhimman kudurori da nufin samar da ci gaba mai ɗore wa, da kuma magance matsalolin da ke addabar mazabar sa da kuma ƙasar baki ɗaya.

"Ga taƙaitaccen bayani kan muhimman kudurorin da Sanata Khalid ya dauki nauyinsu."

“Kowacce Doka an tsara ne domin kawo sauyi mai ɗorewa, da kuma ci gaban Jihar Kaduna da kuma ga daukacin al’ummar Najeriya.”

“Jajicewa a bisa manufar ku, Jagoranci tare da kyawawan Manufa.”

Sanata Ibrahim Khalid

Ayyukansa na majalisa shaida ne ga jajircewar sa wajen inganta rayuwar al’ummar sa da ‘yan Najeriya baki ɗaya. Tun daka fannin ilimi da lafiya zuwa tsaro da shugabanci, kudurorin sa an tsara su ne domin magance manyan ƙalubalen da ake fuskanta a yau, da kuma shimfiɗa tubalin ci gaba mai ɗore wa a nan gaba. Sanata Khalid na ci gaba da aiki tukuru domin cigaban Jihar Kaduna da ƙasar Mu Najeriya baki ɗaya, yana tabbatar da cewa kowanne kudurin doka yana da ma’ana a tafiyar da ci gaban ƙasar mu.